23 Oktoba 2024 - 06:56
Sojojin Yahudawan Sahyuniya Sun Kara Ikrarin Kashe Sayyid Hashim Safiyuddin

Kafar yada labarai ta Al-Arabiya mai alaka da Saudiyya ta yi ikirarin cewa; Kungiyar Hizbullah ta gano gawar Sayyid Hashim Safiyyuddin.


A wanann karon ma sojojin yahudawan sahyuniya sun yi ikirarin kashe shugaban majalisar zartarwar kungiyar Hizbullah Sayyid Hashim Safiyuddin a hukumance a wani hari da suka kai makonni uku da suka gabata.

Kamar yadda Kafar yada labarai ta Al-Arabiya mai alaka da Saudiyya ta yi ikirarin cewa; Kungiyar Hizbullah ta gano gawar Sayyid Hashim Safiyyuddin.

Wadannan da'awar ta sake tasowa yayin da Hizbullah ba ta tabbatar da labarin shahadarsa ba a hukunce zuwa yanzu.